Labarai

MATSALAR TSARO: Yadda Jama’a Ke Kaura Suna Barin Gidajen Su A Jihar Zamfara

Wadannan mutanen Ƴar Matankari ne dake cikin ƙaramar hukumar Anka ta jihar Zamfara bayan da Barayin Daji suka kai musu hari.

Al’ummar yankin suna ta roƙon Gwamnati da ta kai masu dauki da jami’an tsaro kusan sama da ƙwana talatin kenan bayan da wasu yaran Fulani suka yi musu barazanar hana su zama lafiya a yankin.

Shi dai wannan ƙauyen bai wuce tafiyar kilomita ashirin ba daga Anka.

Ko a cikin ƙarshen makon nan an kai hari a Zurmi, inda aka kashe gwamman mutane, wanda har ya ja Gwamnatin Jihar bada dama ga al’ummomi su kare kansu.

Innalillahi wa Inna Ilaihir Raji’un Hasbunallahu wa Ni’imal wakil Allahuma ajjurna fi Musibatana Hazihi Akhlifna Khairan Minha.

Daga Muhammad Aminu Kabir

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button
%d bloggers like this: