Hukumar zabe mai zaman kanta INEC ta kasa a jihar Yobe, ta bayyana cewa barazanar tsaro ce ta tilasta mata dawo da ilahirin cibiyoyin zabe daga karamar hukumar Gujba zuwa Damaturu, babban birnin jihar.
Kwamishinan hukumar a jihar Yobe, Alhaji Ahmad Makama ne ya bayyana hakan ga manema labarai a ofishin sa, tare da karin haske kan cewa, daukar wannan mataki ya zama dole domin kaucewa barazanar rasa rayukan jama’a da sauran kayan zaben.
“sannan kuma mun dauki matakin ne biyo bayan takardar koke da korkfi wadda masu ruwa da tsaki a karamar hukumar suka yi, inda suka bukaci a sauya musu wani waje na daban, ta dalilin wani harin da aka kai satin da ya gabata- tare da nuna rashin gamsuwar su da gudanar da zaben a can”.
“Wanda hakan ya jawo muka dauki matakan bin diddigin matsalar, inda muka bukaci jami’in mu da ke karamar hukumar ya tattaro mana bayanan, wanda kuma daga bisani muka kira taron jami’an tsaro tare da masu ruwa da tsaki a sha’anin zaben, lamarin da a karshe muka cimma matsayar yanke shawarar dawo da cibiyoyin zaben, wadanda ke karamar hukumar Gujba zuwa Damaturu”.
- Advertisement -
“wanda bisa ga wannan ne ya sa ala-dole muka kauro da gundumomin zaben, saboda yadda a harin da aka kai a garin; makon da ya wuce, an ji maharan suna tamnayar a ina ne inda ake yin zabe, saboda haka gudanar da zabe a irin wannan wajen babbar kasada ce”. Inji Makama.
Inda kafin wannan matakin, tun da farko hukumar INEC ta canja ilahirin cibiyoyin zaben da ke fadin karamar hukumar zuwa manyan garuruwa da suka kunshi Gujba, Goniri da Buni-Yadi.
Haka kuma, wannan karamar hukuma itace wadda dan takarar gwamnan jihar- Alhaji Mai Mala Buni ya fito, wanda kuma da farko a can ne zai kada kuri’ar sa.
Bugu da kari kuma, ta dalilin wannan sauyin, ga dukan alamu, jama’a da dama ba zasu samu zarafin jefa kuri’un su ba a wadannan zabuka na 2019.