Labarai

MATSALAR TSARO: Gwamna Matawalle Ya Dakatar Da Sarkin Zurmi Daga Karagara

Daga Isah Abdullahi Dankane
An dakatar da Sarkin ne a bisa dalilin rashin tsaro dake addabar karamar hukumar ta Zurmi dake jihar Zamfara.

Kuma Gwamnan ya nada kwamintin da zai aiwatar da bincike akansa bisa ga tuhume-tuhumen da ake yi masa akan matsalar rashin tsaron.

Wannan dai shine Sarki na hudu da wannan gwamnati ta dakatar kenan.

Shin kowace nasara aka taba samu game da dakatar da Sarakunan da ake yi bisa zargin su kan matsalar tsaro?

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button
%d bloggers like this: