Labarai

Matashi ya kashe kansa ta hanyar yanke al’aurarsa da kwalba

Rundunar ƴan sandan jihar Kano a arewacin Najeriya ta tabbatar da mutuwar wani matashi Mustapha Muhammad mazaunin unguwar Kurna layin Malam Na Andi, da ake zargin ya kashe kansa da kwalba.

Rudunar ƴan sandan ta ce matashin ya yi hakan ne bayan ya kulle kansa a wani gida da ke unguwar Masukwani a birnin Kano, ta hanyar hawa kan gilashin tagar ɗakin gidan ya kulle kansa.

Kakakin rundunar ƴan sandan Kano DSP Haruna Kiyawa ya ce al’amarin ya faru ne a ranar Lahadin da ta gabata, 14 ga watan Fabrairun da muke ciki, bayan samun rahoton cewar matashin ya shiga wani gida a unguwar Musukwani ɗauke da wata fasasshiyar kwalba a hannunsa.

DSP Kiyawa ya ƙara da cewa daga nan sai ya shiga wani ɗaki a gidan ya kuma yanke al’aurarsa da cakawa kansa kwalbar a wurare da dama a jikinsa.

“Jim kaɗan da samun wannan labari ne sai ƴan sanda muka je wannan gida aka ɗauke shi da gaggawa aka kai shi Asibitin Murtala da ke cikin gari, inda ba jimawa likita ya tabbatar da mutuwarsa a yayin da ake ƙoƙarin ceto rayuwarsa,” in ji DSP Kiyawa.

 ɗaya daga cikin matan gidan da ya shiga ya aikata hakan inda ta ce: “Mun tashi da safe muna aiki sai kawai muka ga wannan yaro ya shigo da gudu, bai zarce ko ina ba sai ɗakin mahaifiyata. Sai yake ta bige-bige yana fasa gilasai, muka yi muka yi ya buɗe ya ƙi. Sai aka fasa ƙofar.

“Anan ne fa aka ga ya jijjiwa jikinsa ciwo ya yanke gabansa, jini duk ya ɓata jikinsa.

Usman Umar na daya daga cikin abokan mamacin ya kuma shaida cewar suna tare da matashin sa’o’i kadan kafin ya kashe kansa, kuma ya gan shi ne sanye da gajeren wando ana rikici da shi kan buta.

“Abokina ne tun muna yara, kuma mutumin kirki ne sosai. Na ga suna rigima da wani a kan buta daga shi sai gajeren wando, yana cewa ɗayan ya ba shi butar shi kuma ya hana shi.

“Ƙafarsa duk ya daddauje, jikinsa kuma duk kwata, yana ta cewa tun cikin dare ya fito daga gida so suke su hallaka shi.

“To ni ban san su wa yake nufi ba. Sai na lallaɓa shi na ce ya je gida ya sa kayansa. To daga nan sai ya tafi, ba don haka ba ma da wataƙila a wajen abin zai faru,” a cewar abokin.

Ibrahim Abdusallam ƙanine ga marigayi Mustapha, ya kuma ce ɗan uwan nasu na fama da larurar taɓin hankali wanda a baya bayan dawowarsa daga Saudiyya, kuma kwanaki uku kafin mutuwarsa ciwon nasa ya tashi.

Wannan dai na zuwa ne bayan da aka sami wani ɗalibin Jami’ar FUD da ke Dutsen jihar Jigawa maƙwabciyar Kanon, wanda ake zargin shi ma ya kashe kansa saboda wata taƙaddama da ta shiga tsakaninsa da budurwarsa.

Sulaiman Lawan

Sulaiman Lawan Usman is a graduate in Bsc Mechanical engineering from Kano University of Science and Technology, Wudil. Also a founding member of ArewaBlog. And now he is working with Vision FM Nigeria as Head of engineering

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button
%d bloggers like this: