News

Matashi da ke burin ƙera wa sojojin Najeriya jiragen yaƙi

Wani matashi A Nigeria mai fasahar ƙere-ƙere a Najeriya ya ce ya fara tunanin ƙera wa sojojin Najeriya jirgin sama na yaƙi maras matuƙi ne a lokacin da aka sace ɗaliban sakandiren Kankara su fiye da 300.

Matashin mai suna Ashiru A. Ashiru ya ce ya yi wannan tunani ne domin jami’an tsaron su samu sauƙi a yaƙin da suke yi da ta’addancin a faɗin ƙasar.

Mai Suna Ashiru wanda ke da digiri a ilimin Sifa wato Physics daga jami’ar Alqalam da ke Katsina a arewacin Najeriya ya ce ya yi wannan aiki ne, domin nuna wa duniya irin baiwa da fasahar da Allah Ya yi wa Najeriya.

Matashin ya ce tun yana jami’a yake da sha’awar ƙere-ƙere, inda shi da abokan karatunsa suka ƙera wani ƙaramin jirgin sama mai saukar ungulu Karami.

”A lokacin da aka sace ɗaliban Sakandiren Kankara sai na fara tunanin ƙera wani jirgi maras matuƙi da zai iya gano inda waɗannan ɗaliban suke”, in ji matashin.

About the author

habibjs

Add Comment

Click here to post a comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.