-Advertisement-


Home | Wakokin Hausa | Wakokin Hip Hop | Bidiyos | Kannywood News | Labarai | Dadin Kowa | English News
Advertise With Us | Upload Ur Music
Email:- Send Email

Matasan Kowacce Al’umma Sune Kwalliyar Wannan Al`umma ~ Inji Shekarau


0 351

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Matasan Kowacce Al’umma Sune Kwalliyar Wannan Al’umma ~ Inji Shekarau.

Bayan cece- kuce da zazzafar muhawara da suka biyo bayan wasu kalamai da shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi akan matasan Najeriya a kasar Ingila inda ya ambaci matasan da malalata kuma cima zaune

Tsohon gwamnan jihar kano Dr. Mal.Ibrahim Shekarau yabi sahun ”Yan Najeriya wajen bayyana ra’ayinsa dangane da wancan batu na shugaban kasa a wata hira ta musamnan da yayi a yayin da shashin wasu al’umma suka kai masa ziyara a gidansa .

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 324

- Advertisement -

Mal.Shekarau ya bayyana cewar ko kadan bai yadda da wancan zargi ba duba da cewar matasan kowacce al’umma sune kwalliyar wannan al’umma.

Don haka maimakon shuwagabanni su mai dakai wajen zargin matasa kamata yayi su mai dakai wajen basu kyakkyawar tarbiyya da tallafa musu domin su zamo shuwagabannin al’umma kuma dattawa nagari a gobe.

Mal.Shekarau yaci gaba da cewa “Tunda aka kafa jihohi aka kafa Najeriya ma’aikatun gwamnati ba karuwa suke ba,amma yawan al’umma a kullum karuwa yake.

Don haka batun ma ace gwamnati sai ta bawa dukkan matasa aikin yi bai taso ba
Amma abin tambayar shine ,
shin wane kokari shugabannin al’umma suke wajen bawa matasa tarbiyya da tallafa musu domin dogaro dakai?
Don haka ba daidai bane a dora laifi kacokan akan matasa domin kuwa lalacewar matasa na faruwa ne duba da tarbiyyar da dattawa da magabata suka basu” Inji Mal.Shekarau.

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.