Matar Ganduje ta Kaddamar da Bada Tallafi ga Mutum 530 a Karamar Hukumar Dala

0

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Daga Abubakar Aminu Ibrahim
Mai Girma Umar Gidan Gwamna Dr. Abdullahi Umar Ganduje OFR wato Prof. Hafsat Abdullahi Umar Ganduje ta kaddamar da bada tallafin kudi Naira dubu 20 ga mata 320 da Maza 200 wanda Shugaban Karamar Hukumar Dala ya daukin nauyin basu bisa sahalewar Maaikatar Kananan Hukumomi ta Jihar Kano cikin shirin tallafawa mata da matasa a Karamar Hukumar Dala.

A Jawabinsa Shugaban Karamar Hukumar Dala, Hon Ibrahim Suleiman Dan Isle Dodar ya bayyana cewa wannan shine na farko, don haka Gwamnatinsa zata cigaba da fito da ire iren wadannan tsaruka don tallafawa mata da matasa.

Shima a nasa Jawabin Kwamishinan Kananan Hukumomi na Jihar Kano, Hon. Murtala Sule Garo ya godewa Mai Girma Gwamna bisa yadda yake sahalewa Kananan Hukumomi domin tallafawa Mata da Matasa.

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 732

Anata Jawabin Prof. Hafsat Ganduje tayi kira ga wadanda suka mori wannan Tallafin dasuyi amfani dashi wajen yin sana’a ba aje a sanyasu gaba akashesu ba, sannan ta godewa Shugaban Karamar Hukumar Dala bisa yadda yake jajircewa da rikon amana.

Taron yasamu halartar Shugabar Matar Jamiyyar APC Hajiya Habiba yan Dalla zakanyar Ganduje, SA Fatima Dala yar Amana, Shugabannin Mata na Kananan Hukumomi da sauran Jiga jigan Jamiyyar APC na Karamar Hukumar Dala.

Arewablog Data Bundle Ads

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

%d bloggers like this: