-Advertisement-Home | Wakokin Hausa | Wakokin Hip Hop | Bidiyos | Kannywood News | Labarai | Dadin Kowa | English News
Advertise With Us | Upload Ur Music
Email:- Send Email

Matan Saudiyya Na Zanga-Zanga Kan Sanya Abaya


0

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Wasu daga cikin matan Saudiyya sun gudanar da zanga-zangar adawa da tilasta musu sanya abaya, wadda dogowar riga ce da ke rufe tun daga sama har kasa da suke sanyawa a lokacin da za su fita bayyanar jama’a.

Wannan bore dai na gudana ne a shafukan sada zumunta da muhawara, kuma sun sanyawa maudu’in suna ”sanya abaya a bai-bai”, tare da wallafa hotunan mata sanye da abaya da kuma nikabin rufe fuska wadda suke korafin tana takura musu.

A watan Maris da ya wuce, Yarima mai jiran gadon masarautar Saudiyya Muhammad bin Salman bin Abdul’azeez al-Su’ud ya bayyana cewa sanya doguwar abayar ba tilas ba ne ga matan kasar.

Kusan mutane 5,000 ne daga ciki da wajen kasar suka ta tsokaci kan batun a shafin Twitter.

Wace sutura matan Saudiyya za su sanya?

Gwamman shekaru da suka gabata, hukumomin Saudi na da tsaurin ra’ayi kan suturar da matan kasar ke sanyawa wadda za ta rufe baki dayan jikinsu a bainar jama’a, inda suke sanya abaya matukar musulmi ne.

Amma a watan Maris Yarima Muhammad ya ce mata ba sa bukatar sanya zumbuleliyar rigar, suna bukatar a dama da su a fagen suturar zamani matukar kayan ba sa nuna tsiraici don haka ba lallai sai sun sanya abaya ba.

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 659

- Advertisement -

A wata hira da gidan talabijin na CBS Yariman ya ce “dokokin addinin musulunci a bayyane suke, addinin ya amince mata su sanya tufafin da suka kaimuradi, abu mai muhimmanci shi ne dole su suturta jikinsu, kamar yadda aka umarci maza su aikata hakan.”

Bin Salman ya kara da cewa, “Hakan ba yana nufin lallai sai sun sanya abaya ko bakin nikabin rufe fuska ba. Baki dayan zabi yana ga matan su zabi irin suturar da suke muradin sanyawa.”

Me matan Saudiyya ke wallafawa a shafukan sada zumunta?

Wata mace mai suna Howra ta ce za ta fara sanya abaya a bai-bai domin nuna adawa da dokokin kasarta sannan idan har mata za su fita ba tare da abaya ba hakan na nufin babbar barazana ce gare su ta hanyar bayyanar da kansu ga jama’a.

Howra ta kara da cewa “Ya zama dole mu sanya abaya da nikabi a fuskarmu, saboda kullum abin da ake cewa shi ne muna aiki cakude da maza don haka dole ko ina a jikinmu ya rufu-ruf. Gaskiya wannan abun yana takura mana matuka.”

Shekarun baya da suka gabata dai matan Saudiyya sun fara sanya launuka daban-daban na abaya, ba kamar bakar abaya da kusan a iya cewa suka gada tun iyaye da kakanni ba.

Sannu a hankali suka fara sanya abaya mai budadden gaba da ana iya ganin suturar da suka sanya a ciki kamar wando, ko dogon siket da sauransu kamar yadda wani rahoton kamfanin dillancin labarai na Reuters ya bayyana.

A shekarar da ta gabata ne aka dage haramcin tuka mota da matan Saudiyya ke fama da shi, sai dai har yanzu yawancin matan da suka yi fafutukar tabbatar da hakan na garkame a gidajen kaso a kasar.

Tun daga wancan lokacin ake zargin yarima Muhammad da bada umarnin kashe dan jarida da ya yi kaurin suna wajen sukar yadda yake tafiyar da mulkinsa wato Jamalk Khashoggi a ofishin jakadancin kasar da ke birnin Santambul na kasar Turkiyya, amma Saudiyya ta musanta batun.

Wadanne abubuwa ne har yanzu matan Saudiyya ba za su iya aikatawa gaba-gadi ba?

Akwai abubuwa da dama da matan Saudiyya ba za su iya aikatawa gaba-gadi ba har sai tare da muharammansu, ko dai mahaifi, ko dan uwa, ko kuma mijin aure wasu lokutan ma har da Da.

Daga cikinsu akwai:

  • Neman izinin yin fasfo
  • Tafiya kasar waje
  • Aure
  • Bude asusun ajiya na banki
  • Kasuwanci
  • Yin tiyata yayin rashin lafiya
  • Barin gidan kaso

Batun muharrami kafin mata su gudanar da wasu harkokin rayuwa, ya taka muhimiyar rawa wajen kara wawakeken gibi da rashin daidaito tsakanin maza da mata a yankin gabas ta tsakiya.

Arewablog Data Bundle Ads

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

%d bloggers like this: