Labarai

Mata ‘Yan Gudun Hijira Daga Jihar Borno Sun Buge Da Karuwanci A Jihar Bauchi

Hukumar Hisba a jihar Bauchi ta gano wasu ‘yan gudun hijira daga jihar Borno da suka koma unguwar Tudun Wadan Dan Iya dake jihar Bauchi suke karuwan ci.

Hukumar ta Hisba karkashin jagorancin Barrista Aminu Balarabe Isa ta yi wa matan nasiha tare da jan hankali kan su tuna irin halin da suka fito an kashe musu iyaye da ‘yan uwa maimakon su samu nitsuwa su koma ga Allah sai su shiga aikin fasadi da barna wannan butulci ne da kuma kawowa kansu matsala.

Daga bisani matan sun nuna godiyar su kan yadda aka nuna musu kulawa, kuma sun yi alkawarin cewa a shirye suke a maida su ko kuma a yi musu dalilin samun mazajen aure.

Daga LDB

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button
%d bloggers like this: