Get New DJ Mixes
Labarai

Masu zanga-zangar kin jinin Gwamnatin Buhari sun sha dakyar yau a kasuwar Wuse

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja sun bayyana cewa an samu hatsaniya tsakanin al’ummar gari da masu zanga-zangar kin jinin Gwamnatin Shugaba Buhari a yau Talata.

Masu zanga-zangar ta #Our_Mumu_Don_Do sun yanke shawarar shiga kasuwa neman mutane bayan da suka kasa samun masu mara masu baya.

 

Hausa times ta ruwaito masu zanga-zangar sun kutsa kasuwar Wuse a Abuja suna wake-waken kin jinin Buhari akan lallai shugaban ya dawo ko yayi murabus sanadin da ya tunzura wasu da ake zargin magoya bayan Gwamnatin ne da suka kasa jurewa wannan cin fuska suka mayar da martani.

Bayanai sunce bayan da matasan suka mayar da martani sai hayaniya ta tashi har takai ga an ragargaza motar shugaban masu zanga-zangar mai taken ,“Our Mumu Don Do” mista Charles Oputa (Charlyboy).

Shaidun gani da ido sun bayyana cewa nan take jagoran zanga-zangar ya ruga a guje don ceton rayuwarsa a yayinda dakyar jami’an tsaro suka ceto shi bayan an yita harba barkonon tsohuwa domin tarwatsa gangamin.

Ana dai ganin masu zanga-zangar ne da tsokana domin suna sane cewa kasuwar ta Wuse kasuwace wacce galibinta magoya bayan Gwamnatin dake cine.

About the author

Mr. ArewaBlog

C.E.O/Founder ArewaBlog

Add Comment

Click here to post a comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.