Masu Ta’addanci A Nijeriya Sun Shiga Uku

0

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Daga Datti Assalafiy

Mutuwar tsohon shugaban sojoji marigayi Janar Ibrahim Attahiru gadanga kusar yaki da maye gurbinsa da Janar Faruk tamkar an kashe maciji ne ba’a sare kansa ba

Sabon shugaban sojojin Nigeria Manjo Janar Faruk Yahya ya samu horon soji tun daga farko a bangaren sojoji ‘yan Infantry wato sojojin da ake basu horo na musamman a kan dabarun yakin sunkuru

Janar Faruk Yahaya ya fito daga jihar Sokoto garin mujahidai jikokin Shehu Usman bin Fodio wanda sukayi gadon yaki, gwagwarmaya da jihadi a jinin jikinsu yake

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 773

Abin burgewa garemu Musulmi, Janar Faruk Yahaya Mahaddacin Al-Qur’ani Maigirma ne, ya iya yaren Hausa, Larabci, Faransanci da kuma turanci, kuma yana iya rubutu da duka yarukan

Yana fagen daga a jihar Borno shugaba Buhari ya bashi wannan matsayin, na ga video dinsa lokacin da yake yiwa mayakan sojojinsa bankwana zai taho Abuja, ya yiwa sojojinsa kalaman bankwna masu cike da tauhidi da mika dukkan lamarinsa ga Allah Madaukakin Sarki

Muna rokon Ka Yaa Allah Ka kare shi, Ka bashi taimako, Ka nuna masa hanya mai sauki da zai gusar da ayyukan ta’addanci a Nigeria Amin Yaa Hayyu Yaa Qayyum

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

%d bloggers like this: