Masu Sa Ido Kan Zabe Sun Fasa Kwai: Akwai Barazanar Tada Bam A Masallatai Da Kasuwanni A Kano

0

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Wani rukunin masu sanya ido a harkokin zabe daga kasashen waje ‘Pan African Women Project International Observers’ sun bayyana asirin da suka samu na shirin kai harin bam a wasu wurare garin Kano da kewaye.
Masu sa idon sun bayyana cewa, sun samu sakonnin ‘emails’ daga majiyar da ba za su iya bayyanawa ba inda aka sanar da su cewa, akwai shirin kai hari wani masallaci da kuma babbar kasuwa kafin ranar Asabar da za a gudanar zaben shugaban kasa dana ‘yan majalisar dokokin tarayya.
Sakatariyar watsa labarai na kungiyar, Misis Mphoeue Keitseng, wadda ‘yar kasar Botswana ce, ta bayyana haka a taron hadin gwiwa na manema labarai a garin Kano ranar Talata.
Kungiya ta kuma bayyana cewa, daga tattaunawarsu da masu ruwa da tsaki a harkokin zaben a Nijeriya sun lura lalai rashin sakin kudi da sauri ga hukumar zabe ta INEC ya taimaka wajen matsalkar dage zaben da aka yi a kwanakin baya.
Keitseng ta kuma kara da cewa, “Bayan tattaunawarmu da dukkan bangarorin masu ruwa da tsaki a kan dade zabe da aka yi kwananna, mun lura da cewa:
“Mun fahinci cewa, gwamnatin tarayya Nijeriya bata saki kudade ga hukumar INEC a kan lokaci ba, wanda haka ya sanya ba a samu buga wasu mahimman kayayaki ba a kan lokaci, masali har zuwa yanzu wasu masu sanya ido ba su samu riguna da huluna da kuma sanran abubuwan da ake bukata na gudanar ayyyukansu ba saboda ba a kammala aikinsu ba.
“Na biyu kuma, jihar Kano da kuke gani kamar babu komai, amma mun samu bayanan sirri dake nuna cewa, an shirya kai harin bam a wasu wurare kamar masallaci da kasuwa, za kuma ayi mafani da ‘yan banga don cimma wannna manufar.
“Muna amfani a wannan daman na kira ga gwamnatin tarayyar Nijeriya da ta karfafa tsaro a wuraren taron jama’a kamar su masallatai da cocicoci da kasuwannin.
“daga karshe, bayanin taron manema labarai da aka gudanar a Abuja wadda muma mun samu halarta, zuwa yanzu wasu mahimman kayan aiki sun iso jihohi, amma muna fatan za a gudanar da zaben 2019 cikin nasara.”
Da yake mayar da martini akan yadda suka samu bayanin cewa, hukumar INEC ba ta samu kudaden aiki a kankari ba, ta bayyana cewa, “masu samar da kayyakin suka bayyana mana cewa, ba a basu cikakken kudaden aiki ba har zuwa watan Janairu.”
Da aka tambaye su ko sun mika wadannan bayanan ga jami’an tsaron da suka kamata, shugaban kungiyar a Nijeriya Dakta Uben Udensi, bayyana cewa, “Shigowar mu garin Kano kenan kuma muna shirin mika wa jami’an tsaro wadannna bayanan.
Kungiyar ta kuma bukaci gwamnatin Nijeriya da masu truwa da tsaki su tabbatar da an gufanar da zaben ranatr Asabar cikin kwanciyar hankali ba tare da wani matsala ba.

Wasu Abubuwan Masu Alaka
Talla

Hukumar Karota Ta Kama Mota Cike Da Tabar Wiwi

1 of 661

#Leadership

Arewablog Data Bundle Ads

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

%d bloggers like this: