Labarai

Masu Kwatanta Gwamnatin Osinbajo Da Na Buhari Na Yunkurin Kawo Rabuwar Kawunan Shugabannin ne

Fadar shugaban kasa ta yi Allah tir da yunkurin da wasu mutane ke yi na kwatanta ayyukan da Mukaddashin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ke yi da kuma ayyukan Shugaba Buhari kamar yadda aka san su.
Wani mai baiwa shugaban shawara akan harkokin siyasa, sanata Femi Ojudu shi ya bayyana haka yayin da yake amsa tambayoyin manema labarai a fadar gwamnatin da ke Abuja a yau Litinin.
Ojudu ya bayyana cewa gwamnatin tarayya gwamnati daya ce, kuma babu wani abun kwatance tsakanin shugaban kasa da mataimakin sa, ya ce masu yunkurin yin hakan ‘yan adawa ne masu son haifar da baraka tsakanin shugabannin.
Tun a ranar 19 ga watan janairun shekarar nan ne dai shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bar Nijeriya zuwa Birnin London hutu, inda ya bar ragamar mulkin kasar a hannun mataimakinsa.
Tun bayan tafiyar sa ne, Osinbajo ya fara daukar wasu matakai kwarara, wadanda mutane da dama ke ganin sun fara fitar da kasar daga cikin halin kaka-nikayi da ta samu kanta.
Bangaren da aka fi la’akari da shi shi ne umarnin da Osinbajo ya baiwa babban bankin kasar na yin sauye sauye a manufofin su na hada hadar canji, wanda ke ci gaba da haifar da hauhawa a darajar Naira.