Masu Garkuwa Da Mutane Sun Shiga Hannun Mafusata A Jihar Taraba
An kama wasu daga cikin masu yin garkuwa da mutane a garin Tella Taraba dake karamar hukumar Gassol a jihar Taraba.
Rahotanni sun nuna cewa tsawon lokaci masu garkuwa da mutanen sun addabi al’umma a garin Tella Taraba.
Inda suka
kama mutane da yawa tare da karbar milyoyin kudi.
Sai dai dubun su ya cika a yau, inda matasan garin suka kashe su ba tare da sun mika su ga hukuma ba.
Allah ya kyauta
Daga Rariya
Add Comment