-Advertisement-Home | Wakokin Hausa | Wakokin Hip Hop | Bidiyos | Kannywood News | Labarai | Dadin Kowa | English News
Advertise With Us | Upload Ur Music
Email:- Send Email

Masifar Dake Kannywood Ta Wuce Misali -Adam A Zango


0

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

“Ni ba ‘dan daudu bane kuma ni ba ‘dan maula bane. Sannan ni ba mushiriki bane, bani da malami ko matsafi. Da Allah ka’dai na dogara. Idan kuma akwai malamin da yace na taba zuwa wajansa ko kuma wanda ya taba bani kudi kyauta ba tare da nayi masa aikin komai ba to dan girman Allah kada ya rufa min asiri, tun daga kan ‘yan siyasa, sarakuna, gwamnati, ko masu kudi ko ‘yan mata.

Duk abinda na mallaka arayuwa ta gumina ne ya bani ba dan adam ba. Motar hawa gida ko fili. Dan haka ba wanda ya isa yasa ni inyi abinda banyi niyya ba tunda ba wanda ya taya ni kare mutuncin kare daukaka ta ba.”

“Don haka, hanya daya zaku iya dakatar da daukaka ta, hanyar itace ku dakatar da numfashina. Sai dai kuma kash hakan ba’a hannun ku yake ba. Ku ta yawo dani kuna bata min suna dan Allah ya fifita ni akan ku.

“Kunce min arne kunce min gay (‘dan luwa’di) kunce min mai girman kai, amma duk da haka masoyana ba wanda ya guje ni basu daina sayan fina finai da wakokina ba.

“Haba dan Allah mai nayi muku duk wanda na taimaka a rayuwata sai ya dawo yana yakata”. To na kai bango Billahillazi La’ilaha’illahu duk wanda ya kara taba ni sai na tona masa asiri.”

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 331

- Advertisement -

“Sannan duk wanda ya rufa min asiri akan abubuwan dana lissafa Allah ya tona masa nasa. Ban kira sunan kowa ba a yanzu amma next time zan kira sunan kowaye idan ya kara bata min suna.

Ina da ‘yaya’ ya zama dole na fara kare mutuncin kaina da martabata kafin ya yi affecting din su don Allah kadai yasan gawar fari. Sannan zan ja tunga ga makiyana na kannywood dan hakane kadai za’a banbance tsakanin aya da tsakuwa”

Masoyana ku gafarce ni akan abubuwan dana fada an kure ni ne.

Yadda a ko’ina ake samun nagari da bata gari hakazalika a cikin kannywood akwai nagari da bata gari, kuma wallahi billahi daga yau ba za’a kuma yi min kazafi nayi shiru ba dan kowa a cikinmu yasan kowa. Shi yasa idan akace mana jahilai bana damuwa domin nima nagano hakan. Tunda ance amfanin ilmi aiki da shi.”

#Rariya

Arewablog Data Bundle Ads

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

%d bloggers like this: