-Advertisement-Home | Wakokin Hausa | Wakokin Hip Hop | Bidiyos | Kannywood News | Labarai | Dadin Kowa | English News
Advertise With Us | Upload Ur Music
Email:- Send Email

Masarautar Kontagora Dake Jihar Neja Ta Jaddada Goyon Bayan Ta Ga Sanata Barade


0

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Masarautar ta baiyana hakan ne ta bakin madawakin Kontagora Alhaji Aminu Ahmed a yayin ziyarar girmamawa da Sanatan ya kaiwa masarautar a fadar mai martaba Sarkin Sudan na Kontagora Alhaji Sa’idu Namaska (CON).

Masarautar ta baiyana jin dadin ta akan kudurori na cigaba da sanatan ke kokarin kaiwa a zauran majalisa kama daga matsalolin hanyoyin da yankin ke fama dashi wanda tuni gwamnatin taraiyya tafara gyara hanyar Kontagora zuwa Yauri da bada kwangilar gyaran hanyar Kontagora zuwa Makera da Rijau zuwa Kontagora, da hanyar Kontagora zuwa Bangi, da sauran hanyoyin dake yankin na Neja ta Arewa da babban kudurin dokar kafa jami’ar gwamnatin taraiya a garin Kontagora (Bill for the establishment of Federal University Of Education Kontagora (Est, Etc) Bill 2018 (SB.698) wanda yanzu haka yake dab da samun amincewar majalisa inda za’a turawa wa shugaban kasa domin ya rattaba mashi hannu. 

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 659

- Advertisement -

Madawakin na Kontagora ya kara da cewar “Wannan Masarauta tana goyon bayan Sen.Dr.Aliyu Sabi Abdullahi (Baraden Borgu) dari-bisa-dari yasake komawa domin ya cika burin dake dare shi na alheri, Jama’a mu taya shi da addu’a, mu kuma bada goyon baya da hadin kai, In kuma lokacin zabe yazo mukara zaben shi domin ya cigaba da kawo mana cigaba”, inji Madawakin Kontagora.

Arewablog Data Bundle Ads

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

%d bloggers like this: