Labarai

Masarautar Katsina Ta Dakatar Da Hakimin Kankara, Sarkin Fauwan Katsina

Daga Jamilu Dabawa, Katsina
Fadar mai martaba Sarkin Katsina, karkashin jagorancin mai martaba Sarkin Katsina, Alhaji Abdulmuminu Kabir Usman ta sanar da dakatar da hakimin Kankara, Alhaji Yusuf Lawal.

Jawabin haka na kunshe a cikin wata takardar da sakataren masarautar, Alhaji Mamman Ifo ya sanya wa hannu a yau Juma’a, 30/04/2021.

Takardar ta bayyana cewa dakatar wa ta fara aiki nan take. Amma ba ta bayyana dalilin dakatarwar ba. Karamar hukumar Kankara na daya daga cikin kananan hukumomin da ke fama da matsalar yan bindiga a jihar Katsina.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button
%d bloggers like this: