Labarai

Masarautar Gumel Ta Zartar Da Sabbin Dokokin Neman Aure Da Bukukuwan Aure Baki Ɗaya

DAGA Comr Haidar Hasheem Kano
Masarautar Gumel dake karamar hukumar Gumel a Jihar Jigawa a yau ta ftar da wasu dokoki da ka’idoji na aure a yankin.

Wannan na ƙunshe ne cikin wata takardar sanarwa da aka fitar daga masarautar mai ɗauke da sa hannun Alhaji Murtala Aliyu wanda shine sakataren masarautar Gumel.

Takardar ta nuna wasu dokoki kimanin goma sha tara da masarautar ta ƙayyade kayan da za’ayi amfani da su na Aure da Kuma bukukuwan aure a yankin Masarautar ta Gumel.

Ga Dokokin

1- Ba a kayyade sadaki ba, amma ya zamana yayi dai dai da tattalin arziki al’umma

2- an amince da sanya tufafi guda 6

3- Takalmi guda 3

4- Dan kunne da sarkuna 3

5- Mayafi da hijjabai 3

6- Dan kwali 3

7- Kayan kwalliya saiti 2

8- Kada kudin kayan lefe ya wuce dubu 100,000

9- Yanzu maza kadai aka amincewa sukai kayan lefe

10- An hana kayan nagani inaso

11- An hana kawo kudi ko kayayyakin sa rana

12- An hanayin kayan gara

13- An hana yin kade-kade da suka shafi chakuduwa maza da mata

14- Duk wani bikin aure da za’ayi karya wuce 6 na safe zuwa 6 na yamma

15- Daukar amarya karya wuce 6 na safe zuwa 6 na yamma

16- An hana jerin gwanon motocin kai amarya karsu wuce uku

17- An hana arabiyan night, fulani day, da sauransu

18- Ba ayarda ayi hawan angwanci ba sai da izinin fada

19- Akwai hukunci ga duk wanda ya karya doka

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button
%d bloggers like this: