Wasu marubuta litattafan soyayya na Hausa sun koka cewa, kafofin sada zumunta na zamani suna ci gaba da zama wata barazana ga ayyukansu.
Daya daga cikin marubutan Fauziyyah D. Suleiman da ta rubuta litattafai fiye da 30 ta ce, basa samun makaranta saboda yada ayukansu ta kafofin sada zumunta.
Ta kuma kara da cewa, akasarin mutane su na yada litattafai ta shafuka kamar Facebook da kuma dandalin Whatsapp.
Marubuta litattafan soyayya na Hausa suna da kasuwa sosai musamman tsakanin matasa.
Yawanci suna rubutu ne akan jigon soyayya da zamantakewa, da kuma matsalolin mata.
Kano dai ita ce cibiyar irin wadannan rubuce-rubuce dake haska yadda rayuwar al’umma ke sauyawa.
Add Comment