Adam A Zango Yasha Martani Gun Abokan Sana`arsa Ta Kannywood

1

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Jarumi Adam A. Zango bai bayyana dalilinsa na sauya sheka ba, amma masu lura da al’amuran yau da kullum da ke faruwa a dandalin na Kannywood da wasu abokanan sana’arsa, sun yi ta tsokaci kan wannan mataki da ya dauka.

Sarkin wakan San Kano, Nazir Ahmad, na daya daga cikin fitattun masu nishadantarwa da suka fara mayar da martini kan sauya shekar da Zango ya yi.

Talla

“Ka kira mutane kar su sayar da kuri’arsu, kar su sayar da ‘yancinsu, ka ce ko za a kashe ka sai Buhari….saboda ba a baka kudi ba kawai shi kenan sai lissafinka ya karye sai ka tafi.” Inji Sarkin Nazir Ahmad kamar yadda ya wallafa a wani bidiyo a shafinsa na Instagram.

Ya kara da cewa, “Ku kuna cewa mutane su yi don Allah, ku kuma kuna yi don kudi.”

Sai dai Chizo_1_germany_k, wani fitaccen mai wallafa hotuna da bidiyon barkwanci a shafin Instagram mazaunanin kasar Jamus wanda shi ma a da jarumi ne a Kannywood, ya ce yana ganin, zaluntar Zango aka yi, shi ya sa ya koma PDP.

“Wannan tafiyar da Zango ya canza, wallahi! Wallahi!! yana daya daga cikin zaluncin da ake yi a Kannywood. An san cewa Adam A. Zango masoyin Baba Buhari ne amma sanadiyar kuntata mai da ake yi, ga shi yanzu mun yi losing dinsa (rashin shi), ya bar tafiyar Baba Buhari ya koma tafiyar Baba Atiku.” Inji Chizo_1_germany_k

Adam A. Zango, Allah ya taimake ka.” Chizo_1_germany_k, Chizo ya kara da cewa.

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 331

Ita kuwa Hauwa Waraka, fitacciyar jaruma, cewa ta yi “Mu dai zama daram a APC.

Wani fitacce jarumi da shi ma ya garzaya shafinsa na Instagram ya yi magana shi ne Abba Al Mustapha.​, amm shi lale marhabin ya yi da matakin da Zango dauka.

“Barka da zuwa dan uwa.” Inji Abba wanda ya wallafa hotonsa da Zango suna gaisawa.

Sashen Hausa na Muryar Amurka, ya yi kokarin tsakuro kadan daga cikin irin tsokacin da mabiya shafin Instagram din Zango suka yi, amma ga dukkan alamu ya kulle sashen yin tsokaci.

Yanzu Adam A. Zango, ya hada sheka da jarumai irinsu Sani Danja, Fati Muhammed, Al Amin Buhari, Zaharaddeen, da Teema Makamashi a yi wa Atiku yakin neman zabe.

A gefe guda, Zango ya baro su Ali Nuhu, Sadiq Sani Sadiq, Rukayya Dawayya, Halima Atete, Jamila Na Gudu, Nuhu Abdullahi da Maryam Yahaya a jerin juaramn da ke goyon bayan shugaba Buhari.

Ba a dai taba wani lokaci da jaruman na Kannywood suka samu rarrabuwar kawuna ta fuskar siyasa ba, sai a wannan kakar zabe, kamar yadda masu lura da al’amuran Kannywood ke cewa.

Arewablog Data Bundle Ads

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

%d bloggers like this: