Kannywood

Martani: Naziru Sarkin Waƙa da Aminu Saira ba su da laifi ko kaɗan!

SALAAM mujallar Fim. Na karanta wani labari naku mai taken “Naziru Sarkin Waƙa Ya Hayaƙa ‘Yan Jarida” wanda da dama mutane su ka mayar da martani a kafafen sadarwa, inda su ka bayyana abin da fitaccen mawaƙin ya yi a matsayin tozarci ga ‘yan jarida.

Babu shakka, masu wannan ra’ayi su na da nasu hujjojin, bai kamata a ga laifin su ba, sai dai ni na bambanta da mafi yawan ra’ayoyin nasu. Amma na fi karkata kan ra’ayin Malam Nazifi Dawud, wanda ya nuna yadda ‘yan jaridar da kan su su ke wulaƙanta kan su.

A iya sani na dai, aikin jarida aiki ne mai ɗimbin ƙa’idoji da ‘farillai,’ ‘mustahabbai,’ ‘makaruhai’ da kuma dabaru masu yawan gaske. Muddin har mutum ya kuskure su, ko ya jahilce su, shakka zai faɗa cikin matsala, har ma ya jawo wa kan sa da ma sauran masu sana’ar jangwangwama.

Kan haka ne na ke ganin akasarin masu kiran kan su ‘yan jarida a yau su ke cikin garari.

To, bari mu koma kan zancen da Sarkin Waƙa ya yi a cikin fim. Abu na farko da za mu kalla shi ne labari ne ya bi a matsayin sa na jarumi a cikin shirin. Wanda kuma a farkon farawa ma, wasu gogaggun marubuta ne su ka raba dare, su ka jajirce su ka tsara shi. A cikin su ma, har da ma wasu manyan ‘yan jaridar. Saboda haka, ni ban ga dalilin da za a ɗora laifi kan jarumin ba.

Abin da ya kamata a yi shi ne a fahimci cewar Naziru Sarkin Waƙa fa ‘script’ ɗin labarin ne ya bi, kamar yadda aka tsara, aka ba shi.

A gani na, da yawa daga cikin masu wancan ra’ayin su kan fassara rayuwar mawaƙin ne na zahiri, wanda a ganin su wataƙil zai iya wulaƙanta mutane saboda sun san attajirin mawaƙi ne, wanda kuma hakan babban kuskure ne!

Na biyu kuma masu danganta laifin da darakta Aminu Saira, su ma alwalar tasu ta sami ‘lam’a’. Domin kuwa kafin a shiga lokeshin, sai da marubuta labarin da ma’aikata shirin gaba ɗaya, da ma wasu ƙwararru, su ka zauna su ka yi bitar sa daidai gwargwado.

To, idan mu ka tattaro waɗannan hujjojin, babu yadda za a yi mu danganta laifin ga waɗannan bayin Allah.

Ta yaya za mu kalli aktin ɗin jarumi a cikin fim, mu yanke masa hukuncin zahirin rayuwar sa? Kenan duk labaran da wasu jaruman su ka yi a kan wasu gungun mutane, su ma sai an yi musu hukuncin furucin su kenan? Sau nawa ake nuna gurɓatattun ‘yan sanda a fim? Sau nawa ake nuna alƙalai marasa adalci a wasu kotunan a fim? Shin mun taɓa jin wani ɗan sanda ya fito ya ce an ci zarafin ɗan sanda a cikin fim? Tilas ne a nuna ‘character’ a cikin fim, mai kyau ko akasin hakan, domin wataƙila a cikin fim ɗin har a bayyana wa masu kallo dalilin bijiro da ‘character’ ɗin.

Ba mamaki a cikin fim ɗin za kuma a samar da wani ɗan jaridar da ba ya tsayawa ya karɓi na mota a wulaƙance.
Yanzu bari mu koma zahirin rayuwar wasu ‘yan jarida a wannan zamani. Dukkan mai hulɗa da ‘yan jarida a yau zai yarda da ni cewa Naziru Sarkin Waƙa, ko kuma in ce fitaccen darakta Aminu Saira, sun yi daidai, saboda ko shakka babu akasarin masu aikin jarida sun koma tamkar maroƙa da sunan aikin na jarida.

Mafi yawa ba su da ƙwarewar aiki, sun ɗauka aikin jarida wata dama ce ta tara dukiya ko neman arziki ko ta halin ƙaƙa!

A matsayi na na ƙaramin ɗan jarida, ina ƙyamar masu aikata hakan, kuma wannan lamari da ya faru, ya hasko min wata hanya zan jajirce wajen gina labari kan gurɓatattun ‘yan jaridar, waɗanda a duk san da su ka yi aiki, ba za su kama gaban su ba, sai su koma gefe su na jiran na mota!

Bissalam.

*Malam Al-Amin Ciroma fitaccen ɗan jarida ne, jarumi kuma darakta. Shi ne shugaban gidan talbijim na Farin Waka da ke Abuja

Copright © Fim Magazine. All rights reserved.
www.fimmagazine.com

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button
%d bloggers like this: