MARTANI: Babu Wani Jami`in Dan Sanda Da Ya Kama Ni -Cewar Hadiza Gabon


0 332

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

A safiyar Talata 21 ga Mayu 2019, na karanta wani labari da kafar yada labarai ta jaridar Leadership A-Yau ta buga a shafukan yanar gizonta mai taken ‘Nabaraska Ya Yafe Wa Hadiza Gabon Bayan Ta Durkusa Ta Roke Shi’.

A cikin labarin marubucin labarin mai suna Mustapha Ibrahim ya ce, ‘Jarumi Mustapha Badamasi Naburaska ya yafe wa takwararsa Hadiza Gabon karar da ya kai ta gaban kotun Majistare ta Nomansland da ke Kano, bayan da ta durkusa gwiwoyi kasa ta roke shi a harabar kotu yau Litinin 20 ga Mayu, 2019.’

Ibrahim ya kuma kara da cewa, ‘Bayanan da LEADERSHIP A YAU ta samu sun tabbatar da cewa, jami’an ‘yan sanda sun kamo jarumar ne a Kaduna bayan da kotun majistare da ke zamanta a Kano ta bayar da umarnin damko ta sakamakon kin amsa gayyatar kotun da ta yi.’

Sai dai kash, wani abin mamaki shi ne an wayi gari kamfanin jaridar mai kima da daraja irin Leadership har zai iya yada labaran boge da shaci fadi? A ce wai an kama ni tun daga Kaduna har zuwa Kano, amma babu wani dan jarida ko mutumin Kaduna da Kano da ya ganni a motar ‘yan sanda sai dan jaridar kamfanin Leadership kawai?

Yana da kyau duniya ta san cewa, babu wani jami’in dan sanda da ya kama Hadiza Gabon a garin Kaduna ko a Kano, kai ko ma a Abuja, sabanin yadda rahoton na Hausa Leadership ya nuna! Babu wani abu makamancin hakan, balle har a ce wai na durkusa gwiwoyina kasa na roki Nabaraska a harabar kotun a ranar Litinin.

Abin sani dai shi ne wasu daga cikin makusanmu ni da shi ma kansa Jarumi Nabaraska, suka shiga tsakani, suka nemi da a yafe wa juna saboda zamantakewar tare, wanda hakan ne ya sa har lauyoyinmu suka shaidi yadda aka yi zaman sulhun. Daga bisani kuma lauyoyin da kansu suka kai takardar sulhun kotu, inda alkali ya karanta, kana ya zartar da hukunci.

Kafin ya kori karar, Alkalin kotun Mai Shari’ah Muntari Garba Dandago ya fara ne da janye batun umarnin da kotun ta ba wa ‘yan sanda kan su nemo jarumar duk inda take.

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 317

- Advertisement -

Haka kuma a yayin da yake zartar da hukunci kan karar, Alkali Dandago cewa ya yi, kotu ta yi la’akari da zaman sulhun da bangarorin biyu suka yi, kuma ta yi na’am da hakan. Kana kuma Alkali ya kori karar, sai dai idan har wadda ake karar ta kara aikata wani abu daga bangarena ya biyo bayan yarjejeniyar sulhun da aka yi.

Wannan shi ne ainihin abin da ya faru (akwai kofen takardar hukuncin daga kotun) da aka sanya hatimin kotu da sa hannun alkalin da magatakardar kotun baki daya a ranar 20 ga Mayun 2019.

Tambayar da ya kamata duk wanda ya karanta labarin nan ya yi ita ce, shin me ya sa tun da aka fara zancena, duk rahotannin jaridar Leadership ba sa yi ma ni adalci?

A gaskiya irin wadannan labaran ba su da tushe, kuma sun kauce ka’idar aikin jarida, wanda aka bayyana cewar duk runtsi ya kamata mai rubuta labari ya yi adalci tare da ba wa kowane bangare hakki, amma ta bangarena ba haka yake ba! Leadership ba ta taba kirana domin ta nemi yi mata adalci ba.

Hakan alamu ne da ke nunin cewa ko tantama babu masu buga labaraina a cikin jaridar suna da wasu boyayyun manufofi da suke son su cimma a kan abin da ya shafi Hadiza Gabon. Wanda har haka ne, ashe kenan ba aikin jaridar suka fito yi ba, face kawai su yi amfani da damar da ke hannunsu wajen cimma manufofinsu na rayuwa.

Ashe kenan ya zama wajibi mahukunta kamfanin Leadership da ma kungiyar ‘yan jarida ta kasa da kuma kungiyar editoci da marubuta su fahimci cewa akwai baragurbi a cikinsu, wato mutane da suke yin gaban kansu ba tare bin ka’idojin aikin na jarida ba.

Shi kuwa marubucin labarin da editan jaridan, su fahimci cewa ya zama tilas su fito su bayyana wa duniya gaskiyar lamari, ko kuma a dauki matakan da suka dace a kansu!

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

-Business Advert-

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.