Labarai

Marayu 56,000 aka yi wa rajistan shiga sabbin makarantun gwamnati a jihar Borno

Kwamishinan ilimin jihar Barno Musa Kubo ya sanar da cewa an yi wa marayu 56,000 da suka rasa iyayen su a dalilin aiyukkan Boko Haram rajista a wasu sabbin makarantu 20 da gwamnatin jihar Borno ta gina.

Kwamishinan ya ce gwamnatin jihar za ta ci gaba da biyan kudin makarantan yaran.

Musa Kubo ya sanar da haka ne a taron ‘yan jaridan da aka yi ranar Laraba a jihar.

Ya ce aiyukkan Boko Haram ta hana yara a jihar samun ilimin boko har na tsawon shekaru uku wanda ya sa gwamnatin jihar ta gaggauta gyara makarantun da aka lalata.

Ya kuma ce gwamnatin na gina makarantu irin wadannan a wuraren dake da tsaro ne sannan kowani makaranta na daukar dalibai 2000.

 

Source PMHausa

About the author

Haarun

Co-founder Arewablog

Add Comment

Click here to post a comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.