-Advertisement-


Home | Wakokin Hausa | Wakokin Hip Hop | Bidiyos | Kannywood News | Labarai | Dadin Kowa | English News
Advertise With Us | Upload Ur Music
Email:- Send Email

Manyan Yan Siyasan Da Su Ka Fi Yawan Mabiya A Shafin Sadarwa Na Tuwita (Twitter)


0 359

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Manyan ‘Yan siyasan da su ka fi yawan Mabiya a shafin sadarwa na Tuwita

Jaridar Daily Trust ta fara tattaro bayanin a kwanan nan a yan siyasar da suka fi yawan mabiya (Fallowers) a shafin Tuwita

Shugaba Buhari da Osinbajo sun fi kowa tashe a shafukan sadarwa na Tuwitar

Ga dai jerin manyan ‘Yan siyasar nan da kuma sunan shafin su da yawan Mabiyan su:

1. Yemi Osinbajo

Mataimakin Shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo yana da masu bin sa fiye da Miliyan 1.51 a shafin sa na Tuwita na @ProfOsinbajo.

Farfesan kuma yana bin mutanen da ba su wuce 60 ba.

2. Muhammadu Bhari

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 324

- Advertisement -

Shugaban kasa Muhammadu ne ya ke bin Mataimakin sa a baya a yawan Jama’a a shafin Tuwita da mutane sama da Miliyan 1.4.

Shafin Shugaban kasar shine @MBuhari wanda a da yake daukar @ThisisBuhari.

3. Atiku Abubakar

Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Atiku Abubakar yana da mutane sama da 1, 335, 550 da ke bibiyar sa a shafin sa na @Atiku kuma ya kan yi tsokaci a lokaci bayan lokaci.

4. Nasir El-Rufai

Tsohon Ministan kasar wanda yanzu Gwamna ne ya dade yana amfani da Tuwita kuma yana da mabiya sama da Miliyan 1.32 a shafin sa na @elrufai inda shi kuma yake bibiyar mutane samada 700.

5. Bukola Saraki

Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki yana da Mabiya akalla Miliyan 1.25 kuma dai shi ma ya kan ‘dan yi magana lokaci- lokaci a shafin sa na @BukolaSaraki

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.