Manyan Shuwagabannin Kungiyar izala Sun Jaddada Goyon Bayansu Ga Ganduje

0

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Manyan shuwagabannin kungiyar Izala sun jaddada goyon bayansu ga Ganduje

Shuwagabannin kungiyar Izala reshen jahar Kano sun kai ziyara ga gwamnan jahar Kano a fadar gwamnati jahar, inda suka jaddada masa goyon bayansu ga Gwamna Abdullahi Umar Ganduje, musamman a yayin da yake tunkarar zaben shekarar 2019.

Talla

Majiyarmu ta rawaito cewa shugaban Malaman Izala, Abdullahi Saleh Pakistan ne ya jagoranci tawagar Malaman zuwa fadar gwamnatin jahar Kano a ranar Alhamis 8 ga watan Nuwamba.

A yayin wannan ziyarar da suka kai masa, Malaman sun jaddada goyon bayansu a gare shi, sa’annan suka jinjina ma gwamnan bisa muhimman ayyukan da yake yi a jahar Kano, da ma ayyukan da yake yi ga addinin Musulunci.

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 661

Idan za’a tuna gwamnan jahar Kano ne babban hadimin addinin Musulunci a jahar Kano watau ‘Khadimul Islama’, wanda ko a satin daya gabata sai da gwamnan ya musuluntar da maguzawa da sama da dari biyu.

Sai dai jama’a da dama sun nuna rashin jin dadinsu da wannan ziyara, musamman a wannan lokacin da ake zargin gwamnan da karbar cin hanci da rashawa da suka kai dala miliyan biyar daga hannun wasu yan kwangiloli.

Masu irin wannan ra’ayi na ganin Malaman sun nuna goyon bayandu ga gwamnan a fili, wanda a cewarsu kamata ya yi Malamai su kasance masu daidaita sahun al’umma ba wai su dinga goyon bayan masu mulki akan rashin gaskiya ba.

Arewablog Data Bundle Ads

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

%d bloggers like this: