Wasanni

Man City ta sayi Danilo a kan fam miliyan 26.5

Danilo ya koma Madrid ne daga Porto a shekarar 2015

Kungiyar kwallon kafa ta Manchester City ta sayi dan wasan bayan Real Madrid Danilo a kan fam miliyan 26.5.

Dan wasan wanda dan asalin Brazil ne mai shekara 26 ya rattaba hannu a kan kwantiragin shekara biyar da City ne, kuma zai tafi Amurka ya hadu da sauran ‘yan wasan City da ke can a halin yanzu.

Danilo dan wasa ne mai hazaka, wanda ya na rike baya da tsakiya, kuma shi ne dan wasa na hudu da City ta saya a bana.

 

“Wasu kungiyoyin sun nuna sha’awar siyana, amma na dade ina fatar buga wasa a karkashin Guardiola”, in ji Danilo.

Zuwan Danilo a yanzu na nufin City ta kashe kusan fam miliyan 150 ke nan wajen sayen manyan ‘yan wasa, bayan da ta kammala sayen Kyle Walker (fam miliyan 45), da Bernado Silva dan Portugal (fam miliyan 43), da mai tsaron gida Ederson Moraes, shi ma dan Brazil (a kan fam miliyan 35).

Har ila yau, kungiyar ta cimma yarjejeniyar sayen dan wasan bayan Monaco, Benjamin Mendy da Aleksandar Kolarov, dan wasan baya na kungiyar Roma duka a kan fam miliyan 52.

Amma zuwan Danilo a wannan lokacin na nufin ba zai buga wasan sada zumunta tsakanin City da Real da za a buga a ranar Laraba ba a birnin Los Angeles, har sai ya sami takardun izinin zama a Ingila.

Dan wasan wanda ya taba buga wa Santos ya koma Madrid ne daga Porto a shekarar 2015.

A cikin shekara biyun da ya shafe a Barnabeu, Danilo ya samu nasarar cin La Liga, da kofin zakarun Turai sau biyu, da kuma kofin Uefa Super Cup har ma da wanda hukumar Fifa ke shiryawa na zakarun kungiyoyin duniya.

About the author

Mr. ArewaBlog

C.E.O/Founder ArewaBlog

Add Comment

Click here to post a comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.