Wasanni

Man. City da Chelsea na son daukar Danilo

Danilo ya ci kofin Zakarun Turai a Real Madrid

Manchester City da Chelsea na son sayen dan kwallon Real Madrid mai tsaron baya, Danilo kan kudi fan miliyan 26.

City na son yin amfani da Danilo a matsayin mai tsaron baya da kuma mai wasan tsakiya, ita kuwa Chelsea za ta yi amfani da shi a wajen da take da matsala.

Danilo mai shekara 26, ya koma Real Madrid daga Porto a shekarar 2015, sai dai baya samun damar buga wasa a Real akai-akai.

Chelsea ta amince ta biya fan miliyan 60 kudin Morata na Real Madrid wanda shi ne na hudu da kungiyar ta dauka bayan Tiemoue Bakayoko da Willy Caballero da kuma Antonio Rudiger.