Labarai

Makwabci ya yi karar Sheikh Kabiru Gombe

Wani makwabcin shahararren malamin addinin Musulunci, Sheikh Kabiru Gombe ya gurfanar da malamin a gaban kotun Kofar Kudu da ke birnin Kano bisa tuhumar take hakkin makwabtaka.

Majiyarmu ta ruwaito makwabcin ya zargi Kabiru Gombe da gina maka-makan tagogi a gidansa dake Unguwar Sabuwar Gandu a Kano, wadanda ke ba shi damar leken matan makwabta a zarginsa.

 

Shafin Alfijir ya ruwaito mutumin na cewa “ya sa musu bakin glass ta yadda shi ya na iya ganin cikin gidajenmu amma mu ba zamu iya hangen cikin gidansa ba.”

Makwabcin ya ce tun ana ginin su ka ja hankalin malamin, amma ya ce zai toshe su kafin a kammala, sai dai bai yi hakan ba.

Shafin jaridar Alfijir ya kuma ruwaito a nasa bangaren, lauyan Kabiru Gombe, Ishaq Adam Ishaq, ya ce bakin ciki ne kawai makwabtan suke yi wa malamin saboda daukakar da ya ke da ita.

A yanzu haka dai alkalin kotun, Sarki Yola ya umarci jami’ansa da su je su gano tagogin su dawo da rahoto kafin ci gaba da sauraron karar.

 

Souce In Hausa Times