Makarantu Masu Zaman Kansu Na Barazana Ga ilimin Islamiyya A Kano?

0

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Talla

Makarantu masu zaman kansu na barazana ga ilimin islamiyya a Kano ?
A fahimtata: Gwamnatoci a Kano sun yi sakaci sakaci Sosai akan abin da ya shafi makarantu masu zaman kansu a Kano,an sakar musu linzami suna abin da Suka ga dama,idan kaji mahukunta na kwarbai dasu to maganar daya ce ,batun HARAJI.amma idan ka dauke wannan Babu abin da ake musu.

Sannu a hankali na lura cewa makarantun galiban sun zama Jan wuya,karensu kawai suke ci babu babbaka.

Talla

Amma ni babban abin da ayanzu yafi tayar min da hankali shine yadda makarantun ke zaman Yan mirina a tsakaninsu, yawancinsu sun kirkiri tsarin extra lesson,ko a sanya shi bayan kammala karatu ko kuma a sanya shi a ranakun Asabar.

A fahimtata wannan zai kawo illa akan ilimin addini, domin idan za’a ce yaro zai zauna a makaranta yin lesson to yaushe zai je makarantar Allo ko islamiyya?

Haka ma Asabar idan an ce zaka zo lesson to ya maganar karatun addini?

Talla

Sannu a hankali irin wanna al’ada yado take a tsakanin makarantu masu zaman kansu,kuma da yake extra money ake biya wajen extra lesson din abin ya zama ruwan dare kowacce makaranta sai ta kirkiri wannan fi’ili.nidai anan in baiwa gwamnati shawara da ta dakatar da wannan tsari,me ake yi daga safe zuwa rana ba a koya abin da ya dace ba ?

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 14

Haka ma akwai batun kayan makaranta yanzu wasu makarantun abin Sam Babu tsari an fara mancewa da tsarin hijabi da zani ko dogon sket,an fara komawa dingilallen sket iyakarsa kwauri,sama kuma an saka Riga matsatstsiya (ga dalibai mata) wallahi abin kamar ba a Kano ba,gashi kuma makarantun wake da shinkafa,maza da mata Anya bai kamata a sauya tsarin uniform ba?

Me yasa gwamnati bazata fitar da tsarin kayan da yakamata kowacce makaranta ta sanya ba? Idan fa aka cigaba a haka na tabbata wataran sai abin da aka gani.

Akwai batutuwa da dama,akan abin da ya shafi irin wadanna makarantun Amma hukumar dake lura dasu ga alama tayi sakaci sun fi karfin ta,yadda Suka dama haka za a sha.sun zama hatta uniforms da litattafai sune ke sayarwa.

Nakan rasa dalilin hakan kasuwanci Zasu yi ko bayar da ilimi?

Mutane da dama a yanzu na ta komawa makarantu masu zaman kansu saboda an yanke kauna da na gwamnati,Dan haka nake rokon gwamna da ya wannan tsari a ja kunnen shugaban hukumar lura da makarantu masu zaman kansu a Kano,cewar idan bacci yake ya farka.Zan cigaba insha Allahu

Nasir Zango

Arewablog Data Bundle Ads

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

%d bloggers like this: