Labarai

Majalissar Dokokin Jihar Zamfara Na Neman Mataimakin Gwamna Da Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Su Gurfana A Gabanta

Daga Shattima Jnr
A yau majalisar dokokin Jihar Zamfara a karkashin Jagorancin RT Hon Nasir Magarya, ta cimma matsayar gayato mataimakin Gwamnan Jihar Barista Mahadi Aliyu Gusau da Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Zamfara CP Hussaini Rabi’u domin su gurfana a gabanta a ranar 27-07-2021 don amsa wasu tambayoyi.

Tambayoyin nada alaka da wani gangamin taro da majalissar take zargin mataimakin Gwamnan ya gudanar gangamin taron da take zargin na siyasa an gudanar dashi kwanan biyu da suka gabata duk da cewa a lokacin ana cikin makoki a Jihar sanadiyar kisan da yan bindiga sukayi wa fiye da mutane 50 a wasu tagwayen hare-hare a kauyuka na karamar hukumar Maradun.

A kwanakin baya anrika yada musayar yawu a shafin sada zumunta na facebook na mataimakin gwamnan da kwamishinan Yan Sandan Jihar akan gangamin Taron da Mataimakin Gwamnan ya gudanar

© Zuma Times Hausa

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button
%d bloggers like this: