Majalisar kasa a Najeriya ta tsayar da naira dubu 27 a matsayin karamin albashin ma’aikata a jihohi da kamfanoni da masana’antu masu zaman kansu.
Majalisar ta kuma tsayar da naira dubu 30 a matsayin karamin albashi ga ma’aikatan tarayya.
Shugaba Muhammadu Buhari ne ya jagoranci taron majalisar a fadarsa a ranar Talata wadda ta kunshi tsoffin shugabanni da tsoffin alkalan alkalan Najeriya da kuma gwamnoni da shugabannin majalisa.
Za a mika kudirin ga majalisa a ranar Laraba domin ta amince kamar yadda ministan kwadago Chris Ngige ya bayyana.
- Advertisement -
Ya ce majalisar ta cimma matsayar ne bayan nazari kan matsayar da kwamitin duba bukatar karin albashin ya yanke ta naira dubu 30 da dubu 24 da gwamnatin tarayya ta ce za ta iya biya da kuma naira dubu 22,700 da gwamnoni suka ce za su iya biya.
Karin bayani na tafe..
BBCHAUSA