Labarai

Majalisar Dokoki ta Jihar Katsina tayi karatu na biyu akan gyaran fuska ga kudirin dokar hukumar kula da ma’aikatan majalisar Dokoki ta Jiha

Majalisar Dokoki ta Jihar Katsina tayi karatu na biyu akan gyaran fuska ga kudirin dokar hukumar kula da ma’aikatan majalisar Dokoki ta Jiha.

A zaman majalisar Dokokin na ranar talata 16/05/2023, majalisar tayi karatu na biyu ga kudirin gyaran fuska akan dokar.

Wanda Dan majalisa mai wakiltar karamar hukumar Kaita Hon. Musa Nuhu Gafia ya dauki nauyi gyaran fuska akan dokar.

Gyaran fuskar dokar ya shafi duba kwarewa akan aikin majalisa ga wanda za a nada muka min Akawun majalisa.

Da kuma bin cancanta akan wanda za a nada mukamin Akawun majalisa, da kuma mataima kinsa, da sauransu. Kadan kenan daga cikin gyaran fuskar da za ayi akan dokar.

Duk zaman majalisar na ranar talata karkashin Jagorancin Kakakin majalisar Rt. Hon. Tasi’u Musa Maigari Zango.

Dan majalisa mai wakiltar karamar hukumar Katsina Hon. Aliyu Abubakar Albaba ya gabatar da kudiri na kira ga ma’aikata Albarkatun ruwa ta Jihar Katsina.

Da ta kawo karshen karancin ruwan sha a cikin garin Katsina babban birnin Jihar Katsina, domin rage ma wahalhalu akan neman ruwan amfanin yau da kullum.

Bayan gabatar da kudirin, majalisar ta tattauna sosai akan kudirin, daga karshe majalisar ta amince da kudirin.

Inda Kakakin majalisar ya umurci Akawun majalisar da ya turama majali sar zartarwa ta Jiha domin daukar matakin da ya dace.

16 May, 2023.