Labarai

Majalisar Dattawa Ta Haramta Yanka Jakuna A Fadin Nijeriya

Majalisar Dattawan Nijeriya ta amince da kudurin hana yanka jakuna da kuma safararsu zuwa kasashen waje. Majalisar ta amince da kudurin ne bayan ya tsallake karatu na biyu.

Kudurin wanda shugaban masu rinjaye na majalisar Sanata Yahaya Abdullahi ne ya gabatar da shi wanda kuma ya samu amincewar majalisar a zamanta na ranar yau Talata.

Jakuna suna daga cikin jinsin dabbobi da suka fuskantar barazanar karewa a doron kasa, musamman yadda ake yankawa da sarrafa su a sassan duniya. Masana ilimin gandun daji na cewa dabbobin da aka rayu da su shekaru 1,000 baya yanzu babu burbushin da yawa daga cikinsu.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button
%d bloggers like this: