Labarai

Majalisa Za Ta Amince Da Gabatar Da Gyaran Fuskar Zabe A Makonni Biyu –Lawan

Daga Yusuf Shuaibu,
Shugaban majalisar dattawa, Sanata Ahmad Lawan ya bayyana cewa majalisar kasa tana aiki ba dare ba rana wajen ganin ta gabatar da kudurin gyaran fuskar da aka yi wa bangaren zabe a cikin makonni biyu masu zuwa.

Shugaban majalisar ya bayyaa haka ne a lokacin rantsar da Mista Abimbola Yusuf a matsayin babban kwamishinan hukumar jin korafe-korafen jama’a da kuma wasu kwamishinoni 37 daga jihohi 36 gami da babban birnin tarayya Abuja.

Lawan ya roki al’ummar Nijeriya wadanda ba su gane ko kuma ba su aminta da gyaran fuskar ba da su je kai tsaye ko su aika wakilansu zuwa wajen hukumar na karbar korafe-korafe domin a duba kafin a gabatar da kudurin nan da sati biyu.

“Majalisar kasa suna shirin gabatar da kudurin da aka yi wa dokar zabe gyaran fuska nan da sati biyu ko kuma a cikin sati biyu.

“Abu ne mai matukar muhimmanci ga duk wadanda suke ganin suna da abun cewa ko wani abu da za su iya yi na yi wa dokar zabe gyaran fuska da su nemi dan majalisar wakilansu ko kuma dan majalisar dattawa su gabatar masa da korafinsu.

“A nan zan yi amfani da wannan in bayyana cewa babban jami’in zabe ba shi ne zai bayyana abun da za a yi a gaba.

“A saboda haka abu ne mai matukar muhimmanci a nan wurin hukumar amsar korafe-korafe ta rika yi wa al’umma bayanin halin da ake ciki.”

Haka kuma ya tabbatar da cewa hukumar karbar korafe-korafe ta taimaka wa majalisar kasa wajen magance matsalolin da suke sarke wa majalisar musamman wajen wayar da kan jama’a.

“Muna aiki tukuru domin ganin an warware matsalolin da suke damun hukumar, wanda babban matsalar hukuma shi ne kudi”.

Shugaban majalisar ya ce miliyoyin ‘yan Nijeriya ba su da masaniyar ayyukan hukumar sai su nemi kwamishinan hukumar ya rika bayanin ayyukan hukumar a kafafen yada labarai.

A nasa bangaren kuwa, shugaban majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila ya bayyana cewa hukumar karbar korafe-korafe na kasa, hukuma ce da ake bukata wajen samun ‘yanci Da’adam da wulakanta Dan’adam da cin zarafi.

“Ire-iren wadannan ayyukan su suka tilasta bude wannan hukuma a shekarar 1975 wanda aka sake mata fasali a shekarar 2004.

“Baban dalilin kafa wannan hukumar shi ne a kawar da dukkanin wadansu rashin adalci da danniya a ayyukan gwammanti.”

Femi Gbajabiamila ya nemi sababbin kwamishinonin da su yi iya bakin kokarinsu wajen sauke nauyin da ya rataya a kansu na kare hakkokin gwamnati da na ma’aikata da ‘yan Nijeriya ba tare da nuna bambancin kabilanci ko na addini.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button
%d bloggers like this: