Labarai

Majalisa ta baiwa Buhari shawarar dauko sojojin haya

Majalisar wakilan Najeriya ta baiwa gwamnatin kasar shawarar amfani da sojojin haya wajen shawo kan matsalar boko haram da ‘Yan bindigar da suka addabi jama’ar kasar suna kashewa ba tare da kaukautawa ba.

Wannan na daga cikin kudirori guda 19 da Majalisar ta amince da su bayan taron masu ruwa da tsaki da ta gudanar akan matsalolin tsaron da suka addabi Najeriya da niyar shawo kan su, inda ta mikawa shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Majalisar ta bukaci shugaban kasar da ya gaggauta nazari dangane da tasirin wannan shawara na dauko sojojin hayar wadanda a shekarun baya suka taimaka wajen kakkabe mayakan boko haram a wasu yankunan Jihar Borno.

Rahotan da Majalisar ta gabatarwa shugaban kasa ya kuma kunshi samar da horo ga Yan Sandan kwantar da tarzoma 40,000 domin tinkarar matsalar yaki da ‘Yan ta’adda da kuma tura 1,000 daga cikin su kowacce Jiha domin kai daukin gaggawa duk lokacin da ake bukata, yayin da suka bada shawarar tura sauran zuwa Yankunan Arewa maso Gabas da Kudu maso Gabas da Kudu maso Yamma dake fama da matsalar tsaro.

Yan majalisun sun kuma bada shawarar samar da hanyar samun bayanan gaggauwa dangane da matsalar tsaro a kowanne yanki da kuma samar da na’urorin daukar hoto da tauraron ‘dan adam akan manyan hanyoyin kasar da wuraren taruwar jama’a da manyan biranen Najeriya da kuma kan iyakokin kasar.

Majalisar ta kuma bada shawarar samar da kwamitocin tsaro a yankunan kananan hukumomin Najeriya 774 a karkashin jagorancin Rundunar Yan Sanda ta kasa wanda zai kunshi Sarakunan Gargajiya.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button
%d bloggers like this: