A yau ne Gwamnan Jihar Kebbi Sanata Abubakar Atiku Bagudu ya yanka sabon katin rijistar katin zama memba na jam’iyar APC a mazabarsa ta Nasarawa II a Runfar Malam Mai Alelu dake Birnin Kebbi mai lambar 006.
Kuma daga yau an fara yin rijistar katin zama Memba a jam’iyar APC a jihar Kebbi. Inda ake gudanar da yin rijistar katin a karkashin kwamitin jam’iyar APC na kasa karkashin jagorancin Farfesa Sani Yahaya.
Daga Zaidu Bala Kofa Sabuwa Birnin Kebbi.