Labarai

Mai Yiwuwa Na Fito Takarar Shugaban Kasa A 2023, Cewar Gwamna Yahaya Bello

Daga Comr Abba Sani Pantami
Gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello ya ce yana duba yiwuwar amsa kiran da ake yi masa na fitowa takarar shugabancin kasa a babban zaben shekarar 2023.

Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin zantawa da ya yi da manema labarai a gidan gwamnati bayan ganawarsa da Shugaba Muhammadu Buhari a ofishinsa a fadarsa ta Aso Rock Villa da ke Abuja.

Ya kuma ce cancanta da kwarewa a aiki ne ya kamata a yi amfani da su wurin zaben shugaban kasa na gaba, ba kabilarsa ko yankin da ya fito ba.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button
%d bloggers like this: