Get New DJ Mixes
Android Labarai

Mai Girma Gwamnan Kano Ya Halarci Bikin Kwamitin Fitar Da Burtali Ga Makiyaya

Mai Girma Gwamnan Jihar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje OFR Khadimul Islam ya halarci bikin kaddamar da
Kwamitin Fitar Da Burtali Na Masu Kiwon Shanu na Kano saboda ci gaba da kaucewa rigima tsakanin Fulani da Makiyaya, wanda ke karkashin shugabancin Manajan Daraktan Hukumar Bunkasa Aikin Gona Da Raya Karkara Ta Jihar Kano (KNARDA), Ibrahim Sulaiman Dan Isle.

Wanda a ka yi a farfajiyar Hukumar KNARDA dake kan Titin Hadeja a Birnin Kano.

Ya kuma kaddamar da rarraba motoci guda 5 da kuma Babura saboda rarrabawa ga malaman gona wanda shirin Majalisar Dinkin Duniya na UNDP da Hukumar KNARDA su ka samar. Ya kuma kaddamar da tsarin noman rani na shinkafa na shekarar 2020 zuwa 2021..

Abba Anwar
Babban Sakataren Yada Labarai Na Gwamnan Jihar Kano
Asabar, 17 ga Watan Oktoba, 2020
[email protected]
[email protected]

About the author

Haarun

Co-founder Arewablog

Add Comment

Click here to post a comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.