Labarai

Mahajjatan Nigeria na cikin mawuyacin hali a Saudiyya

Wadannan na cikin wasu hotuna dake yawo a kafafen yada labarai cewa mahajjatan Nigeria na zube cikin rashin lafiya a harabar masallacin sarki Abdulazeez dake Makkah.

 

Hausa times ta ruwaito daga rahotannin cewa mahajjatan na fama da zazzabi daban-daban amma hukumar kula da aikin hajji ta Nigeria ta yasar dasu babu wata kulawa na asibiti ko magani.

Hausa times ta yi kokarin tuntubar hukumar kula da ayyukan hajji amma abun ya faskara sakamakon suna ta jigilar mahajjata.

Muna fata idan sun natsu zasu binciki wannan rahoto domin yin abunda ya dace.

Ko ya kuke gani jama’a ?

About the author

Mr. ArewaBlog

C.E.O/Founder ArewaBlog

Add Comment

Click here to post a comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Advertisement