Gwamnatin kasar Amurka ta lashi takobin karfafa Demokradiyya a Najeriya amurka tace Gudunmuwar da zata iya badawa shine sanyawa duk wanda aka samu da magudi takunkumi Da dama daga cikin yan siyasan Najeriya na da gidaje da dukiya a Amurka sai dai basu da damar zuwa.
Cikin wadanda Gwamnatin Amurka ta hana zuwa kasar ta sakamakon zargin su da magudin zabe Akwai Gwamnan jihar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje sai Gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai da Gwamnan Kogi Yahaya Bello da kuma tsohon shugaban APC Adam Oshiomole.
Majiyar Jaridar Amintacciya ta tabbatar mata cewa ko a jiya Gwamnatin Amurka ta fitar da sanarwa mai dauke da sa hannun mai magana da yawun ma’aikatar wajen Amurka, Morgan Ortagus da ya fitar cewa ta haramtawa wasu yan siyasa a Najeriya shiga kasarta daga yanzu saboda zargin rashawa ko magudin zabe.
Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje; yana ciki sai gwamnan jihar Kogi, Alhaji Yahaya Bello.
Shi kuma gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa’i, an tsawaita haramtawar da akayi masa tun a baya.
A cewar jami’an kasar Amurka, za’a kara sunayen wasu yan siyasan Najeriya cikin jerin wadanda aka haramtawa shiga kasar bayan zaben jihar Edo idan sukayi magudi.
Gwamnatin Amurka ta fadi cewa an turawa yan siyasan da aka hana sanarwar hakan ta hanyar Email.
Add Comment