Ministan Shari’a, Abubakar Malami ya zargi Shugaban Hukumar EFCC, Ibrahim Magu na gurgunta shirin gwamnatin tarayya na kawo karshen cin hanci da rashawa a Nijeriya ta hanyar amfani da bayanan sirri ba bisa ka’ida ba.
Kakakin Ministan, Salihu Usman ya ce yadda Magu ke sarrafa bayanan sirri ya janyo aka cire Nijeriya daga cikin kasashen kungiyar nan da ke kare bayanan sirri na kasa da kasa wato ‘ Egmont Group’.
An dai jima na takun- saka tsakanin Ministan da kuma Shugaban EFCC bayan da shi Magu ya ki mikawa Ministan rahoton zargen rashawa da ake yi Akan wasu tsoffin gwamnoni.
‘Souce In Rariya’
Magu Na Gurgunta Shirin Yaki Da Rashawa – Ministan Shari'a

Add Comment