Magoya bayan Buhari na gangami cikin ruwan sama
Dandazon magoya bayan shugaba Buhari sun isa Aso Rock Villa a gangamin da sukeyi domin nuna goyon bayansu ga shugaban.
A yanzu haka dai ana shatata ruwan sama kamar da bakin kwarya amma bai hana matasan cigaba da wake-wake da kade-kaden nuna goyon bayansu ba.
Hausa times wacce ke wajen ta ga tsubin jami’an tsaro yan Sanda da na farin kaya suna Santa ido domin tabbatar da ba’a karya doka ba
Add Comment