Get New DJ Mixes
Labarai

Magidanta Na Bada 'Yan 'yansu Ga Boko Haram Don Aikata Kunar Bakin Wake

“Magidanta Na Bada ‘Yan ‘yansu Ga Boko Haram Don Aikata Kunar Bakin Wake”.
Daga Haji Shehu
Rundunar sojan Nijeriya ta gargadi iyaye da masu rike da sarautun gargajiya akan wani rahoto da ta samu akan yadda iyaye ke bada yayansu ga kungiyar Boko haram don aikata kunar bakin wake.
Rahoton wanda Usman Kuka Sheka ( SK Usman) kakakin rundunar sojin Nijeriya ya wallafa a shafinsa na sada zumunta na cewar, rundunar su ta samu wannan rahoto ne bayan nasarar kame wasu yan kunar bakin wake da tayi.
 
Magidantan na bada yayansu a matsayin gudun mowa ga aiyukan Boko haram, sannan daga bisani suce yayansun sun bata ne.
Rumdumar ta hori al’umma da su kasance masu sanya ido akan yankunansu, sannan su kai rahoton duk wani mutumin da basu yarda dashi ba ko rahoton duk mutumin yayansa suka bata ko aka daina ganinsu yanzu haka.
Har ila yau rundunar ta ce ba ta dakatar da bada tukuicin naira dubu dari biyar (500,000) ga duk wanda ya bada rahoton dan kunar bakin wake ba, kuma kofa a bude take ga duk wanda yake da rahoto kan yan kunar bakin wake zai iya kiran wannan lamba 193 daga ko wacce layin salula.

About the author

Mr. ArewaBlog

C.E.O/Founder ArewaBlog

Add Comment

Click here to post a comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.