Labarai

Magidanci Ya Yiwa Babbar Kawar Matarsa Juna Biyu, Ta Sha Alwashin Sai Ta Haiho Jaririn

Shiri Ya Kwabe: Magidanci Ya Yiwa Babbar Kawar Matarsa Juna Biyu, Ta Sha Alwashin Sai Ta Haiho Jaririn

daga Sharif Lawal Wata budurwa ta yanke shawarar ƙin rabuwa da mijin babbar ƙawarta bayan ta ɗanɗani zumar sa ta ji yadda ya ke Hakan dai ya fara ne bayan babbar ƙawarta ta bayyana girman kayan aikin mijinta, inda ita kuma tace bari ta tabbatar da kanta Sai dai, ta samu juna biyu kuma ta sha alwashin sai ta haiho jaririn, inda ta ke cewa ba haka ta so ba, ita ta so ne kawai su more juna da shi.

 

Auren wata matar aure yana tangal-tangal bayan, mijinta ya yiwa babbar ƙawarta ciki. Wata mai yin kwalliya mai suna @Queenyetty1 wacce ta bayar da labarin a Twitter, ta tabbatar da cewa lamarin ya auku da gaske.

Acewarta, matar auren da babbar ƙawarta sun kalli wani bidiyo ne wanda ya nuna girman kayan aikin mazaje.

Mijin babbar ƙawarta ya yi mata ciki Hoto: Igo Alecsander, FG trade Asali: Getty Images Sai abin ya birge budurwar, inda tace abinda aka nuna a cikin bidiyon ba gaske ba ne.

Matar auren sai ta bayyana cewa ta yarda ƙarya ne, amma akwai maza masu irin wannan, kuma mijinta yana ɗaya daga cikin su.

Wata shida bayan aukuwar hakan, kawai sai budurwar ta samu juna biyu tare da mijin ƙawarta, sannan ta sha alwashin ƙin zubar da cikin ko rabuwa da mijin ƙawarta.

“Yanzu ƙawarta mai juna biyun ba ta son zubar da cikin ko rabuwa da mijin. Tace ba haka ta so ya faru ba, ta so ne kawai ta ɗanɗana shi kawai a wuce wajen.” A cewar mai yin ƙwalliyar.

‘Yan soshiyal midiya sun yi tsokaci @Olayemiariyike ta rubuta: “Sharrin mata kenan. Abin kunya da takaici ga mata.

Matar auren ita ma tana da laifi. Meyasa za ta yi magana kan kayan aikin mijinta har ta riƙa tallar su ga ƙawarta? Ai yanzu ga shi nan ta ga sakamako, ko fara mo.”

@mogdalene ta rubuta: “Duk wani abu da ya danganci saurayina ban yin maganar a gaban ƙawayena, bai ma san ƙawaye na ba.

” @Multi__Face ya rubuta: “Meyasa za ki riƙa tallar abinda mallakin ki ne ke kaɗai?” Iyalai Sun Baiwa Hammata Iska Kan Kudin Sadakin Diyarsu N250,000 A wani labarin na daban kuma, hatsaniya ta ɓarƙe a tsakanin wasu iyalai bayan an kawo kuɗin sadakin ɗiyarsu. Kuɗin sadakin N250,000 waɗanda surukinsu ya biya, sun janyo har sai da suka ba hammata iska a tsakaninsu.

About the author

habibjs

Add Comment

Click here to post a comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.