Magidanci ya dabawa matarsa mai ciki wuka da yayanta

0

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

undunar ƴan sanda jahar Kano ta tabbatar da kama wani magidanci da zargin saran matarsa mai ciki wata goma da yayanta bayan da wata kotu ta raba aurensu.

Yan sanda sun ce sun kama shi ne bayan da suka jiyo kururuwar tsohuwar matar tasa da aka raba auren nasu a ranar Litinin din makon da muke ciki, bayan ta nemi dauki.

Abin ya faru ne a karamar hukumar Rano lokacin da matar ta kai karar mijin da ke cin zarafinta, dalilan da suka sanya alkali raba auren.

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 693

Matar mai suna Shafa’atu Sale ta ce an kammala shari’ar ba jimawa mijinata ya bi ta da wuta ya ɗaɗɗaɓa mata.

Yanzu haka dai Shafa’atu na kwance a asibitin Rano tana karban kulawa, yayinda su kuma jami’an tsaro ke zurfafa bincike.

Wannan dai ba shi ne karon farko da ake samun irin wannan korafi ko zargin cin zarafi da magidanta ke aikatawa a kan matarsu ba a Kano.

Arewablog Data Bundle Ads

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

%d bloggers like this: