Labarai

Maganar Gaskiya Yaran Abba Kyari Suna Karbar Cin Hanci

Magana Ta Gaskiya Ko Abba Kyari Ba Ya Karbar Cin Hanci, Yaran Sa Suna Karba
Daga Faisal Mayolope, Taraba
Na taba rubutawa shugaban Miyetti Allah na kasa Alhaji Bello Bodejo doguwar wasika akan irin cin zarafi da karbar milliyoyin kudade da yaran Abba Kyari suke karba a hannun Fulani da sunan beli, inda ya yi min alkawari zai yi bincike.

Irin miliyoyin kudade da yaran Abba Kyari suka karba a hannun Fulani a jihohin Taraba, Nasarawa, Adamawa, Plateau da Benue ba za su misaltu ba.

An yarda idan aka kama mai laifi a yanke masa hukunci ko na kisa ne wannan ba damuwa. Amma sai su kama wanda bai ji ba bai gani ba su azabtar da shi kuma su sa a tara miliyoyin kudade a tura musu. Wannan ba daidai bane.

Daga karshe Abba Kyari fa ba Mala’ika bane shi Dan Adam ne zai iya yin kuskure.

Idan yana da gaskiya Allah ya fidda shi.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button
%d bloggers like this: