– Siyasa da dangantaka na tsami tsakanin mazhabobin APC a jihar Kano
– Yan darikar Kwankwasiyya na zargin gwamna Ganduje da tadiya
– Kwankwaso ya yi hobbasa don ilimin yara a kasashen waje
A ci gaba da ake da kokarin katse karatun dalibai wadanda tsohuwar gwamnati ta tura karatu kasashen waje, wadanda basu kai maki da gwamnati ta kayyade ba, mutan kwankwasiyya na gani wannan tadiya ce domin tasgaro ga tafiyar kwankwasiyya zuwa 2019.
A baya ma dai, sai da tsohon gwamnan ya garzaya kasar masar domin kokarin cetar daliban guda 37 wadanda ke karantar likitanci da Nas-Nas, a jami’ar Al-Mansoura a kasar ta Masar.
A cikin yara dari da 160 dai a makarantar, gwamnatin Kano ta gaza biyan kudaden makarantar wadanda basu kai maki 2 cikin biyar ba, inda ta ce bata da isassun kudade.
A yanzu dai mabiya Kwankwaso sunyi kira ga shugaba Osinbajo da shugaban APC domin a samu a shawo kan gwamnan kada yayi kiranyen. Kwamared na Kwankwasiyyar ta kasa dai, wadda ke kiran kanta da garkuwar Kwankwasiyya a kudancin Najeriya, Ikonomwan Francis, yayi wannan kiran ne inda yace ai da gwamna Ganduje aka yi shawarar a wancan lokaci. A 2019 dai ana sa rai Sanata Kwankwaso zai so ya kayar da Gwamna Ganduje a tazarce.
Souce In Naij
Add Comment