Get New DJ Mixes
Kannywood

Ma’anar Hollywood, Bollywood, Ghollywood Da Kannywood

Ma’anar Hollywood, Bollywood, Ghollywood Da Kannywood

*Martani Ga Sheikh (Allama) Muhammad Bin Uthma

Daga Mubarak Umar

Na san da yawa za su kalubalance ni duba da taken rubutuna, sai dai ‘gaskiya ko ta kare ce a ba shi kayarsa.’
Wani rubutu yana zagayawa shafukan Facebook, WhatsApp da Instagram, kuma ana alakanta shi da Sheikh Muhammad Bin Uthman, cewar ya yi ta’arifin ma’anar sunayen masana’antun shirya fim na duniya.

Sai dai abinda ya ja hankali bai wuce yadda nake ganin kamar an sanya son zuciya wajen bayar da ma’anonin wood-wood ba. Idan na so, zan iya cewa waccan magana ba zata fito daga bakin Malam ba, amma an tabbatar min da ya yi ta.

 

A lafazin da aka ce Malam ne ya yi, an nuna kamar wadancan sunayen sun munana matuka, har ma ana nuni da cewar, suna nufin fasikanci, fajirci, iskanci ko kafirci.

Mun riga mun san tun bayan mulkin mallaka, harshen turanci ya yi tasiri kwarai a zamantakewarmu, ta yadda wasu abubuwan da yawa ba mu da su a harshen Hausa, sai dai mu aro.
Saboda haka zan yi bayani ma’anar wadancan kalmomi da kuma dalilin samar da su a takaice, idan hali ya yi, zan fadada.

Hollywood = Asalin Kalmar ba ta nufin dandanlin shirya finafinai na Amurka ba ne, illa iyaka wani bigire da yake da ciyawa/fulawa mai kyawun gani, wadda aka fi samunta a iya wannan yanki.
Mun riga mun san Kalmar (wood) a kan kanta ta nufin (itace) ne, ko kuma katako. Saboda haka, wannan bigire a wancan lokaci yana da yalwar katakwaye.

H. J. Whitley, shi ne ya sanyawa wannan wajen Hollywood, tun babu halitta dan adam a wurin. Saboda haka, ma’anar da aka ba ta a wancan ta’arifi ya sha bamban da yadda yake a zahiri.

Bollywood = Kasancewar turawa sun taka rawa sosai wajen assasa masana’antar fim, kamar yadda suka yi abubuwa kamar haka; Mulkin Mallaka, Dimokuradiyya, Boko, Jirgi, Mota, Allura, Sirinji da sauran abubuwa. Shi ne ya sanya masana’antar shirya finafinai ta kasar Indiya, wadda a shekarun 1940s ake ce mata ‘Hindi Cinema’ ta ari suna Hollywood, ta cire Holly, ta san Bolly, wanda shi kuma Bolly an samo shi ne daga Bombay, watau babban Birnin Indiya a da, kafin ya mayar da suna garin Mumbai.

Haka yake Ghollywood, Tollywood har zuwa kan Kannywood. Amma abin da wasu ba su sani ba shi ne, akwai manyan masana’antun shirya fim da ba su sanya wood a sunansu ba. Misali, kasar England, ana kiran ta da British Film Industry, ba Londwood ba.

Haka yake a Kannywood, kamar yadda muka aro kalmomi sun fi dubu daga turawa, muke amfani da su a maganganunmu na yau da kulluma, masu shirya fim din Hausa, sai suka yi amfani da sunan Kano, aka samar da Kan(o)nywood.

A sanin da na yiwa Sheikh, mutum ne mai tsananin bincike kan harkokin rayuwa, wadanda suka shafi addini da wadanda ba na addini ba. Saboda haka, ina ganin kamata ya yi kafin a rika bayar da irin wannan fatawa, yana da kyau a zurfafa bincike, domin irin wannan zai iya sa mabiya Malam suka rika kallon masu sana’ar fim da wani irin bahagon ido (musamman da aka jingina abin kafirci/cultism), wanda zai iya kai wa ga tayar da hargitsi, ko kuma kyama a tsakanin mutanen da suke zaune a unguwa daya, gari daya, kuma kasa daya.

Idan har za mu aro, January, February, March, April, May, June, July, August, September, October, November, December, mu rika amfani da su a lissafin wata; mu sanya a wayoyinmu, kalanda a gidajenmu, ban ga laifin aro Kalmar wood, da Kannywood ta yi ba.

Mubarak Umar
07037934034

About the author

Mr. ArewaBlog

C.E.O/Founder ArewaBlog

Add Comment

Click here to post a comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.