Labarai

Ma’aikatan Gwamnatin Zamfara Sun Gudanar da Sallah ta Musamman Kan Rashin Biyan Albashi

Ma’aikatan Gwamnatin Zamfara Sun Gudanar da Sallah ta Musamman Kan Rashin Biyan Albashi

Wasu ma’aikatan gwamnati a jihar Zamfara sun gudanar da sallah ta musamman a masallacin Idi da ke Gusau babban birnin jihar a ranar Asabar. Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Ma’aikatan da suka yi dandazo a masallacin da misalin karfe 10 na safe sun nemi daukin Ubangiji kan matsalar rashin samun albashinsu.

Ma’aikatan dai sun ce an biya su albashi na karshe ne a watan Janairu, kuma suna fuskantar matsi wajen biyan bukatunsu.

“An matsa wa wasu daga cikin sun koma mabara, ba mu iya cin abinci ko sau daya a rana. Don haka, muka shirya wannan Sallah, wata hanya ce ta musamman don neman daukin Allah da ya bai wa mai girma gwamna, shugaban ma’aikata, ‘yan majalisar tarayya da duk wanda abin ya shafa, ikon tausaya mana.

“Mun sha wahala sosai saboda wannan gwagwarmaya, da yawa sun rasa rayukansu kuma muma ba ma son hakan ta same mi. Mun taru ne don neman taimakon Allah kan lamarin,” in ji daya daga cikinsu da ya nemi a sakaya sunansa.

Kokarin jin martanin gwamnatin jihar kafin hada wannan rahoto ya citira domin layin wayar kwamishinan yada labarai Ibrahim Dosara akashe take.

About the author

habibjs

Add Comment

Click here to post a comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.