Lyrics

[Lyrics] Nura M Inuwa Sabuwar Sirrin Ruhi

Download Song

Ita- Sirrin Raina Zana Fada Mai Sona Zauna Na fadama Sirrina Na Fadama Sirrina Ga Sirrin Ruhina

Shi- ayy Inaji Rirrin Ruhinki To Kaina Zan kamawa Fadan maganar Soyayyata Yatakene A Cikin Ranki

Ita- Ayy To Kaji Sirrin Ruhina Abunda Nakeson Zanawa Gyara Zama Sabon Zance Soyayya Zan Nunama

Amshi- Inkaji Sirrin Ruhi Ya Mutu Kauna Ce A Cikinsa Ga Masanan Masana Zance Soyayya Mahadin Kauna

Shi- Ayy Sonki Yana Yawo A Cikin Raina

     Anfa Ji Sirrin Ruhi
Shi- Kanki Nake Kakame Harshena

    Anfa Ji Sirrin Ruhi
Shi- Taso Zoki Tsayawa gefena

    Anfa Ji Sirrin Ruhi
Shi- Ki Furici In Banda Hakikarshi Bancewa Wallahi

Amshi- Inkaji Sirrin Ruhi Ya Mutu Kauna Ce A Cikinsa Ga Masanan Masana Zance Soyayya Mahadin Kauna

Ita- Ayy Kai Na Rike banayin Hange

    Anfa Ji Sirrin Ruhi
Ita- Fili Da Zuci Nayima Bege

    Anfa Ji Sirrin Ruhi
Ita- Jin Dadin Tafiya Shine Waige

    Anfa Ji Sirrin Ruhi
ita- Zana Riqeka Na ma Ladabi Karikeni Dan ‘Dan Abdullahi

Amshi- Inkaji Sirrin Ruhi Ya Mutu Kauna Ce A Cikinsa Ga Masanan Masana Zance Soyayya Mahadin Kauna

Shi- Ayy Kanki Dikan Haqi Zan Karewa

    Anfa Ji Sirri  Ruhi
shi- Duk Yanayi Na Zama Zan Jurewa

    Anfa Ji Sirrin Ruhi

Shi- Gunki Hawaye Zan Shasharewa

    Anfa Ji Sirrin Ruhi
Shi- Mai Hakuri Shine ke Dacewa In Nabiyo Tarihi

Amshi- Inkaji Sirrin Ruhi Ya Mutu Kauna Ce A Cikinsa Ga Masanan Masana Zance Soyayya Mahadin Kauna

Ita- Ayy Duk Wata Soyayya Zan Nunama

     Anfa Ji Sirrin Ruhi
Ita- Inka Zuro Igiyarka Na Kakkama

   Anfa Ji Sirrin Ruhi
Ita- Ka Kamo Kifi Acikin Koma

    Anfa Ji Sirrin Ruhi
Ita- Nayi Bayanina Dalla-Dalla Baka Bukatar Sharhi

Amshi- Inkaji Sirrin Ruhi Ya Mutu Kauna Ce A Cikinsa Ga Masanan Masana Zance Soyayya Mahadin Kauna

Shi- Kanki Na Kare Dik Soyayyata

    Anfa Ji Sirrin Ruhi
Shi- Ke Zan Alkinta In Ririta

   Anfa Ji Sirrin Ruhi
Shi- In Nanufo Fuskarki Ki Sassauta

     Anfa Ji Sirrin Ruhi
Shi- Ki Fara,a Fuska Tai Nunawa Sai Naji Sanyin Ruhi

Amshi- Inkaji Sirrin Ruhi Ya Mutu Kauna Ce A Cikinsa Ga Masanan Masana Zance Soyayya Mahadin Kauna

Ita- Ayy Nashiga Nayi Nutso Acikin kauna

   Anfa Ji Sirrin Ruhi
Ita- Gaskiya Zanafadi Ba Kin-Kina

   Anfa ji Sirrin Ruhi
Ita- Kai Daya Nanuwa Dangina

    Anfa Ji Sirrin Ruhi
Ita- Gaske Abin Da Yazo Yai Shudewa Za Ayiwa Tambihi

Amshi- Inkaji Sirrin Ruhi Ya Mutu Kauna Ce A Cikinsa Ga Masanan Masana Zance Soyayya Mahadin Kauna

Shi- ayy Inaji Rirrin Ruhinki To Kaina Zan kamawa Fadan maganar Soyayyata Yatakene A Cikin Ranki

Ita- Ayy To Kaji Sirrin Ruhina Abunda Nakeson Zanawa Gyara Zama Sabon Zance Soyayya Zan Nunama

Amshi- Inkaji Sirrin Ruhi Ya Mutu Kauna Ce A Cikinsa Ga Masanan Masana Zance Soyayya Mahadin Kauna

Rubutawa Abubkar Rabiu KanoGurus

Yi Comment Don Mugane Yayi Muku

About the author

Mr. ArewaBlog

C.E.O/Founder ArewaBlog

Add Comment

Click here to post a comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.